ALAMOMIN TASHIN ALQIYAMA.
Kashi na 5.
121 Alkiyama bazata tashiba sai anyi watsi da
musulunci, ba karatu ba aiki.
122 Alkiyama bazata tashi ba sai an dauke
Alkur'ani mai girma daga cikin takardu, da kirjin
mahaddata,
123 Wata bataliyar mayaka zasu tunkari macca da
niyar yaki, amma kasa zata hadiye su a hanya.
124 Zaa kauracewa zuwa aikin hajji.
125 Kabilar kuraishawa zasuyi kadan a duniya.
126 Rushe kaabah ta hannun wani mutum daga
yankin Habasha.
127 Wata iska mai dadi zata dinka dauke ran
muminai idan musifa tayi yawa.
128 Zaa dinka yin ginai- ginai masu tsawo a
Macca.
129 Wasu tsinannun mutane, zasu dinka laantar
magabata, (Annabawa).
130 Zaa sami kayan hawa na zamani,
131 Bayyanar Ma'hadi,
Zamu ci gaba a darasi na 6, kuma insha Allahu
zamu dauki daya bayan daya domin sharhi da
karin bayani, duka wadananan alamomi wadanda
suka zone acikin ingatattun hadisai, na sunnah
(Allah yasa mucika da imani)
Home »
ALAMOMIN ALQIYAMA.
» Alamomin Tashin Alkiyama 5.
No comments:
Post a Comment