Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

Alamomin tashin Alqiyama 4.

ALAMOMIN TASHIN ALKIYAMA (4).
Mun tsaya akan alama ta 100, zamuci gaba.
101 Bayyanar bakar fitina gama gari sai ta shafi
kowa.
102 masifu za suyi yawa birni da kauye.
103 Wani zamani zaizo sujjada daya tafi duniya da
abinda yake cikin ta, saboda karancin masu ibada.
104 Rigima akan ganin wata, saboda wata zai
kumbura, ya dinka fiyowa babba.
105 za a dinga kaura ana komawa yankin Sham
wato Syria.
106 Yakin duniya tsakanin musulmi da Rumawa
(Turawa).
107 Zaa bude yankin Qusdunsuniyya, karo na biyu,
bayan na zamanin daular Usmaniyya.
108 Zaa dena rabon gado, (masu karfi su cinye na
kanana).
109 Zaa dena farin ciki da samun ganima (saboda
wadata tayi yawa)
110 Zaa koma amfani da makamai na gargajiya,
saboda na zamani zasu dena amfani.
111 Zaa raya baitul Maqdis, bayan karbo shi daga
hannun yahudawa.
112 Mutane zasu kauracewa Madina, idan shagala
tayi yawa.
113 Madina zata kore ashararai daga cikin ta, babu
mai jin dadin zaman madina sai mumini.
114 Duwatsu zasu gushe daga gurinsu, saboda
gine-gine naci gaba.
115 Wani mutum zai fito daga yankin Qahdan na
larabawa kuma mutane zasu bishi.
116 Bayyanar wani mutum mai suna Jah,Jah.
117 Dabbobin dawa zasuyi magana irin ta mutane,
kamar zaki da kura da makaman tansu.
118 Tsumagiya ma zatayi magana,(Bulala)
119 Hancin takalmi zaiyi magana.
120 Jikin mutum zaiyi magana (kamar cinyarsa)
tabashi labarin abin da iyalansa suke aikayawa
idan bayanan.
Allah kasa mucika da imani.
Zamuci gaba darasi mai zuwa.
Insha Allah.
Share:

No comments:

Post a Comment

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate