Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

SIRRIN ZAMA DA MIJI 9B

mamatan-kwarai.jpg

SIRRIN ZAMA DA MIJI

{KASHINA 9}

(IYA MAGANA 2)


BY

MUHD*ABBA*GANA
09039016969

manzon Allah yana cewa mafi alherin aure shine auren da aka samu sauki a cikinsa koba komai dukkan iyayen da suke bukatar nemawa yayansu girma a idon mazajensu to sai ku kyautatawa mijinta tare da nuna mishi ai shima dansune don haka dole ne su kyautata masa. to amma abin haushi kuma abin takaici sai ya zama mafi mafi akasarin hankalin iyaye ya tafi a cikin sai an yiwa yayansh abinda zasuyi alfahari da shi kuma su burge koda kuma shi mijin zai shiga halin damuwa da takaici, wanda idan muka dubi koyarwar manzon Allah ya nuna cewa koda a cikin harkar saye da sayarwa Allah yana yin rahama da jin kai a gurin dan kasuwar da yake saukaka kayan siyarwarsa to ballantana ma a cikin sha,anin aure wanda yake duk wanda yace yana son yarka tofa baka da kamarsa a cikin masoyanka don haka shine mafi cancanta da a taimaka masa tare da yin agaji da tausayi a gare shi to amma abin mamaki sai yazo a halin da muke ciki yanzu babu abinda ake jira face sai wanda za,a dorawa nauyi. to jama a ya kamata mu riki koyarwar manzon Allah da kuma abinda zai janyo mana farin ciki da zaman lafiya da sukuni a tsakanin junanmu wannan shine zai taimaka izuwa dorewar zamantakewar aure. kuma ya kamata mu sani cewa shifa auren nan ibada ne bai dace ba a ce muna shigar da son zuciyarmu a cikin abin da Allah ne ya tsara ga yanda yake so aiwatar dashi. in da ace tsadar aure ko kuma tsadar tsadaki wani abin alherine ko kuma wata daraja ce a gurin Allah madaukakin sarki to da mafi cancantar wadanda ya kamata suyi hakan, to amma saiya zama a tsakaninsu bbu tsanantawa sai fa jin kai da tausayi da rahama a tsakaninsu. don haka idan har ba za mu iya yin yanda sukayi ba to sai mu kamanta domin mu samu kadan daga darajojin da suka samu. muna rokon Allah ya hadamu da mata ba gari wadanda zasu taimake mu domin cikar addinin mu ya Allah kayi a gaji ga dukkan matan da suke yin biyayya a gurin mazajensu da kuma wadanda suke taimakon mazajensu kafin na kammala wannan littafi ina sanar da dukkan madmsu sha'awar karanta littafina cewa ina masu albishir da fitowar sabon littafina mai suna "UWA TA GARI" muna rokn Aah yayi mana ludufi da kuma mafita a cikin dukkan al,amuranmu 'amin. NI MARUBUCIN WANNAN LITTAFI INA DADA YIWA ALLAH GODIYA DAYA BANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFI WANDA YA TATTARO MUHIMMAN DARUSA DA SUKA SHAFI RAYUWAR MA,AURATA MUSAMMAN YANDA YA KAMATA AMARYA TAYI MU'AMMALA DA MIJINTA A MUSULUNCI INA ROKON ALLAH YAYI MANA JAGORANCI A CIKIN DUKKAN AL,AMURANMU'AMEEN SUMMA AMEEN DAN UWANKU MUHD ABBA GANA
09039016969

hanyantsira.mywapblog.com
Share:

No comments:

Post a Comment

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate