Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

SIRRIN ZAMA DA MIJI 4

SIRRIN ZAMA DA MIJI
{KASHINA 4}
(TSAFTA)
BY
MUHD*ABBA*GANA 09039016969
Tsaftarki itace mafi amfani a cikin tsarin
mu'amalarki da mijinki,dukkan biyayyar da zakiyi
masa to ki sanifa tsafta itama wata muhimmin yar
abace da zata taimaka domin kammalar jin dadi a
tsakaninku, yazo a cikin hadisi cewa manzon Allah
(SAW) yace mafi alheri mace itace wacce ake
samun farin cikiyayin da aka kalleta, wato itace
wacce take farantawa mijinta yayin da yake
kallonta, ko ba komai ita tsafta itace cikar imanin
mutum don haka ba daidai bane a gurin matar
aure a sameta cikin kazanta, tsaftan ya kunshi
gurin kwanciya, yayanta, dakinta,abinci, jikinta,
gashin kanta, hakoranta,farcenta dukka wayannan
abubuwa ya kamata a ce mata sun kiyaye. yazo
acikin wani hadisin manxon Allah (SAW) yana
cewa: mafi alherin mace itace wacce idan aka
kusanceta sai aji kamshi yana tashi a tare da ita
( ba wani warin albasa albasa ba) don haka ashe
ya isa abin kuna a gurin mace aji wari da doyi
yana tashi a jikinta,domin ita kan tama bazata ji
dadin kanta ba ballantana shi wanda yake tare da
ita wato mijinta. toh abin da ya sawwaka kenan
Allah bamu ikon gyarawa baki daya.Ameen.
Share:

No comments:

Post a Comment

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate