SIRRIN ZAMA DA MIJI 7
SIRRIN ZAMA DA MIJI {KASHINA 7} (KIYAYE DUKIYARSA) BY MUHD*ABBA*GANA 09039016969 yazo a cikin siffofin salihar mace cewa manzon Allah (SAW) yake cewa: ita ce matar da take kiyaye kanta kuma ta kiyaye dukiyar mijinta a lokacin da yake a gida da kuma lokacin da baya gida. don haka dukkan mace ta gari itace wacce take kiyayewa tare da taimakawa mijinta a cikin sha'anin tattalin arzikinsa. bayan haka yana da kyau mace ta kare kanta daga barin yawaita tambayar mijinta domin aikata haka yana janyo mata zubewar kwarjininta a idon mijinta don haka yana da kyau mace ta kiyaye wadannan abubuwa domin samun kyakkyawar zamantakewa mai aminci a tsakaninta da mijinta. Allah ya baku ikon gyarawa, naku har kullum jikan marubuta muhd abba gana
No comments:
Post a Comment