SIRRIN ZAMA DA MIJI
{KASHINA 5}
(KAUNAR MIJI)
BY
MUHD*ABBA*GANA 09039016969
yazo a cikin hadisi cewa "matayen ku wadanda
suke matukar kaunarku anan duniya sune matayen
da zaku zauna dasu a cikin aljannah (mallam
ammafa sai aiki mai kyau) kuma a nan soyyaya
sifface ta yan matan aljannah don haka ko anan
duniy managartan mata ne kawai zaka ga suna
nuna w mazansu soyayya domin mafi akasarin
wasu matan suna ganin idan wai suka nuna wa
mazansu kauna ai sun zubar da ajinsu, kuma wai
sai na miji ya raina su. wannan wani rashin
tunanine da kuma rashin ilimi ne da yayi wa wasu
matan yawa, domin yazo a cikin wani hadisi cewa:
idan miji ya kalli matarsa yayi farin ciki da wannan
kallon to wannan matar zata kasance a cikin
mafifitan mata a lahira" to yaya kuma a matsayin
ita matar da take nunawa mijinta kauna tare da
faranta masa? amusulun ci ana so mace ta dauke
hankalin mijinta ta hanyar dadada masa domin kar
ya fita waje matan banza su dauke hankalinsa.
abin da ya sawwaka kenan Allah baku ikon
gyarawa, ameen naku har kullum har abada jikan
marubuta muhd abba gana
No comments:
Post a Comment