Manya Manyan Aiyyukan Zunubi
DAGA ZAUREN
HANYAN***TSIRA
ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .
WADANNE AYYUKANE SUKAFI KOWANNE AIKI GIRMAN ZUNUBI ?
Abdullahi dan Mas'ud yace:Wata rana na tambayi Manzon Allah (S.A.W) nace:Ya Manzon Allah a Duk cikin laifukan da ake yiwa Allah wane laifi ne yafi kowane laifi girman Zunubi a wajan Allah (s.w.t) ?Sai Manzon Allah (S.A.W) yace:
1. Ka sanya wa Allah kishiya (Shirka) Alhalin Shi ya halicce ka shi kadai. Sai Abdullahi dan Mas'ud yace tabbas wannan
babban al'amari ne.
Sai kuma me?
2. Manzon Allah (S.A.W) yace:Ka kashe danka don kar yaci abinci tare dakai a
rayuwa, dan kar kadauki da wainiyarsa.
Sai Abdullahi yace:
Sai kuma me?
3. Manzon Allah (S.A.W) yace:Kayi Zina da matar makwafcin ka.Yan Uwa kunji a duk cikin laifukan da yafi girman zunubi a wajen Allah bayan shirka.Bayan ita sai Kisan kai, ba wani laifi da ya kai lafin
Zina a musulunci girman zunubi.
Duk wanda ya dauki zina amatsayin sana'a, ko a matsayin aikin yi toh Wallahi ya gaiyato fushin Allah akan sa, kuma yana sone ya jefa Al'umma acikin masifa cikin bala'i, kuma zai gamu da
masifu, zai gamu da bala'i zai gamu da walakanci tun a duniya kuma zaiyi mum munan karshe, a
lahira kuma zai gamu da azaba mafi muni.
Allah ya kare mu daga aikata wadan nan manyan laifuka, ya kuma karemu daga sharrin shaidan,Allah ya shiryemu baki daya.
www.hanyantsira.mywapblog.com
09039016969
Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like
https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/
وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
No comments:
Post a Comment