LIMAMINMU YA MANTA AYA DAYA A FATIHA ?
DAGA ZAUREN
HANYAN***TSIRA
LIMAMINMU YA MANTA AYA DAYA A FATIHA ?
Assalamu alaikum, malam barka da qoqari.Mal. Ya matsayin sallar da liman ya tsallake aya
guda a cikin fatiha ???
Jazakallah.
(Daga Halliru abdullahi)
AMSA.
=======================
ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.To dan'uwa Annabi (s.a.w) yana cewa:"Babu sallah ga wanda bai karanta fatiha ba"kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta:723.Malamai sunyi sabani akan Idan liman ya manta
aya daya a Fatiha, a sallar da take ta farilla, bai tuna ba, sai bayan yayi sallama, wasu malamai sukace zaiyi sujjadar rafkannuwa.
Amma zance mafi inganci shine:Idan har ba'a samu lokaci mai tsawo ba, to sai yatashi yasake raka'a daya.Idan kuwa an samu tazara mai tsawo tsakanin
lokacin daya tuna da kuma lokacin sallamarsa, to
zai sake sallar ne gaba dayanta, saboda fatiha
rukuni ce ta sallah bata tsayawa sai da ita, kamar yadda hadisin daya gabata yake nuni.Domin neman Qarin bayani sai aduba Fatawaa
Alajna Adda'ima:5/331.
Allah shine mafi sani.
www.hanyantsira.mywapblog.com
09039016969
Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like
https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/
وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
No comments:
Post a Comment