Wadanne gurarene aka Haramta mace takalla ajikin 'yar uwarta mce ?
DAGA ZAUREN
HANYAN***TSIRA
ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .
Malam menene hukuncin mace tabayar da jikinta
ga mata yan’uwanta don ayi mata wanka saboda kwalliya ko irin dilka da halawa din nan wai haramunne Koda ta rufe mamanta da mazaunanta ?Idan haramun ne kenan daga ina zuwa inane
tsiraicin mace da bai kamata yar’uwarta mace ta gani ba ?
Jazakallahu khairaljazaaa.
(Daga Murjanat Sunusi).
AMSA
-------------------------------------------
ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.To ‘yar uwa malamai sunyi sabani gameda tsaraicin mace ga ‘yar’uwarta musulma.
Akwai wadanda suka tafi akan cewa:
1- Bai halatta ‘yar uwarta mace taga wani abu a jikinta ba, sai abin daya saba bayyana a tsakanin
mata.Idan suna zaune isu-isu, kamar kafa da hannu da fuska da wuya da makamacin haka.
2. Saidai abin da mafi yawan malaman fiqhu suka tafi akai shine:
Al’aurar mace ga ‘yar uwarta musulma tana farawa ne daga cibiya zuwa guiwa, kamar yadda al’aurar maza take a tsakaninsu.
Don haka bai hallata tabari wata mace takalli samada wannan wurin da aka iyakance ba.
3. Amma idan kafira ce matar to malamai sunyi bayani cewa bazata kalli wani abuba, sai abin da
yasaba bayyana, don haka sai a kula lokacin da za’aje dilka wajan wacce ba musulma ba, don kada garin neman gira a rasa ido .
Sannan a bisa wannan bayanin da kikayi, dilkar da kika siffanta zata zama bata halatta ba, tunda za’a
ga abin da shari’a bata hallatata a gani ba.
WALLAHU A'ALAM
www.hanyantsira.mywapblog.com
09039016969
Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like
https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/
وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
No comments:
Post a Comment